Ana bikin na Babbar Sallah ne yayin da dimbin Musulmin da suka samu sukunin zuwa aikin Hajji a kasar Saudiyya, ke kammala aikin na Hajjin.
Bayan kammala sallar idin dai musulmai masu hali za su yanka dabbobin layya.
A lokutan sallah dai jama'a na kai ziyarce-ziyarce ga 'yan uwa, gami kuma da rabon abinci da ake yi na musamman.
A bana dai bukuwan sallar na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Nijeriya ke fama da matsi na tattalin arziki, abin da ake gani zai iya rage armashin sallar a wajen wasu, musamman wadanda ba su damar yin layya ba.
Malaman addinin musulunci dai na kiraya-kiraye ga wadanda suka samu halin yin layyar da su taimaka wa wadanda ba su samu ikon yi ba da naman layya.